Connect with us

DAGA JIHOHI

ƘUNGIYAR AYCMF TA GUDANAR DA TARUKA A JIHOHI SHIDA 22/5/2022

Published

on

KUNGIYAR MATASAN AREWACIN NIGERIA “AREWA YOUTHS CONCERN MEDIA FORUM” (AYCMF) TA GUDANAR DA TARUKA A JIHOHI SHIDA 22/5/2022.

 

Daga Kungiyar: Matasan Arewacin Nigeria “Arewa Youths Concern Media Forum” (AYCMF)

 

Tarukan sun gudana a jihohin Bauchi Borno Kaduna Gombe Kano Sokoto. anyi taron ne domin wayar wa yan uwa matasa kai dangane da halin da Arewa da al’ummar Arewa suke ciki da kokarin nunawa matasan mu muhimmancin hadin kai domin magance wasu daga cikin matsalolin matasan na arewa.

 

Taron ya maida hankali wajen kokarin nunawa matasa muhimmancin hadin kai a tsakanin mu domin tunkarar matsalolin yankin mu da dukkan karfin mu mussamman abunda yake ci mana tuwo a kwarya wato ta’addanci. kungiyar AYCMF ta tattauna sosai akan hanyoyin da za abi a dakile tunanin ta’addanci a kwakwalen matasan mu masu tasowa.

 

Kungiyar AYCMF tana fafutukar hada kan matasan Arewa a jihohi 19 da Abuja 20 domin mu zama tsintsiya madaurinki daya. masu magana da murya daya. karkashin inuwar Kungiyar domin cimma kyawawan manufofin ta guda biyar (5) da take aiki akai.

 

Kungiyar AYCMF tana maraba da dukkan wani matashi Namiji ko Mace mai kishin Arewa da al’ummar Arewa. kuzo mu hada kai domin samar da cigaban matasan mu a cikin kasar mu Nigeria. ayyukan kungiyar AYCMF yana fantsama lungu da sakon Arewacin Nigeria muna bukatar karin dakaru domin tabbatar da kyawawan manufofin kungiyar.

 

Kofar wannan kungiya abude take ga dukkan wani matashi mai kishin Arewa da al’ummar Arewa. kuzo mu hada kai domin dawo da martabar yankin mu da al’ummar mu a idon duniya.

 

Allah ya zaunar da Arewa lfy ya hada kawunan mu. mu zama tsintsiya madaurinki daya.

Sign:

AYCMF MANAGEMENT

22/5/2022

DAGA JIHOHI

EFCC Na Zargin Tsohon Gwamnan Kano

Published

on

Daga Mujahid Wada Musa Kano

hukumar da ta ke yaki da hana cin hanci da rashawa EFCC ta garkame wani kango da kuma asibitin da ke jikinsa a unguwar Bompai ,mallakin tsohon gwamnan jahar Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.

Tsohon gwamnan yana fuskantar zargi ne daga wasu ƴan fansho inda suka shigar da kararsa a shekarar 2015.
Asibitin da hukumar ta EFCC ta garkame din shi ne wanda ya bawa gwamnatin jahar Kano a lokacin da cutar corona ta fara kamari akasarnan dan killace masu fama da ita amma gwamnatin Kanon bata karba ba.

Sai dai wasu rahotanni mai kwanan watan 27 ga watan mayu na 2015 kwankwaso ya karbi gudunmawar naira miliyan 70-saba’in daga kananan hukumomi 44 na jahar Kano da jumullar kudi ya kai sama da biliyan 3 dan yakin neman zabensa na takarar shugaban kasa a 2015.

Continue Reading

DAGA JIHOHI

Ƴan bindiga sun hallaka ‘sama da mutum 35’ a jahar Zamfara

Published

on

By

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun kashe sama da mutum 40 a jerin hare-hare da suka kai a wasu kauyukan jihar.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da kai harin, amma ta shaida wa BBC Hausa cewa mutum 35 aka kashe.

Lamarin ya faru ne a ƙauyuka fiye da biyar da ke karamar hukumar Maradun da ranar Alhamis sai dai bayanai ba su fito ba sai Juma’a.

Ganau sun shaida wa BBC cewa maharan sun je ƙauyukan Gidan Adamu da Gidan Maidaji da Bauci da Wari da Kyara da Gidan Maidawa kan babura sannan suka buɗe wuta.

Lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum 42, a cewar wani mutum da muka tattauna da shi.

“Wannan lamari ya faru ne a jiya Alhamis tun daga karfe 12 na rana har zuwa bayan la’asar, a lokacin da ‘yan bindigar suka shiga shiyyar kan babura sama da 100,” in ji wani da ya shaida lamarin.

Wannan hari na zuwa ne kwana biyu kacal bayan da ƴn bindiga suka kashe mutum 18 a jihar Katsina.

Sannan kuma waɗannan hare-hare duk sun faru ne a yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin cetofiye da ɗalibai 100 da aka sace a wata makarantar kwana a jihar Kaduna.

Satar ɗaliban ita ce ta baya-baya cikin lamari irin sa da yake neman zama ruwan dare a arewacin Najeriya.

Continue Reading

DAGA JIHOHI

Bethel Baptist High School: ‘Yan bindiga sun sace ‘dalibai 150’ a jihar Kaduna

Published

on

By

Bayanai sun tabbatar da sace dalibai da dama a wata makarantar sakandare da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeirya.

Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a sakandaren Bethel Baptist High School, Damishi da ke Karamar Hukumar Chikun da asubahin Litinin tare da sace dalibai da dama.

Kamfanin dillancin labaria na Reuters ya ambato mahaifin wani dalibi yana cewa kusan 150 ne ba a gani ba bayan harin da ‘yan bindigar suka kai.

Sai dai hukumomi sun ce sun ceto mutum 26 daga cikin wadanda aka sace.

Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph Hayab, wanda ya tabbatar wa BBC Hausa labarin, ya ce dansa yana cikin daliban makarantar amma ya kubuta.

Duk da yake ba a san adadin daliban da aka sace ba, Rabaran Hayab ya ce a ranar Juma’a mun kirga “dabilai 180 da suke ɓangaren kwana amma a safiyar nan yaran da muka samu ba su fi 24 zuwa 27 ba”.

“Muna sa ran dai waɗannan ɓuya suka yi a wani wuri amma dai waɗancen an tafi da su,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Da ma ranar Juma’a an yi ganawa da malamai tun da abubuwa [na rashin tsaro] suna faruwa ko za a cire yaran daga makaranta.

Sai dai Rabaran Hayab ya ce jami’an tsaro sun yi wa makarantar kawanya.

Amma a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige ya fitar ta ce “jami’anmu sun fafari ‘yan bindigar ta hanyar amfani da dabaru da makamai kuma sun yi nasarar ceto dalibai 26 ciki har da wata malama guda daya cikin koshin lafiya.

Ana ci gaba da neman dukkan daliban domin tabbatar da cewa an ceto su cikin koshin lafiya,” a cewarsa

Yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun kashe mutum bakwai a ƙarshen mako a Jihar Kaduna.

A ranar Asabar Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya cire ɗansa daga makarantar gwamnati saboda ‘yan fashi na ynƙurin sace shi.

Maza da mata
Makarantar ta Bethel Baptist High School ta ƙunshi maza da mata sannan kuma akiwa waɗanda ke kwana da kuma masu zuwa kullum.

“Ɗana da aka ɗauka namiji ne amma wanda ya faɗa mani labarin ya ce ‘yarsa aka ɗauka, sai dai sun kuɓuta tare,” a cewar Mista Joseph Hayab.

Ya ƙara da cewa yaran da suka kuɓuta suna hannun hukumar makaranta ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Continue Reading

BABBAN LABARI

Copyright © 2020 VOA voiceofarewa.ng