Connect with us

NISHADI

Akwai bukatar maza su kara aure – Dr Idris Ahmad

Published

on

Fitaccen da fafutuka nan kuma shugaban kungiyar gwagwarmaya ta CUUP  wanda ya kware wajen kera motacin guje-guje Dr. Idris Ahmad ya bada shawarar cewa akwai bukatar maza su kara aure ganin abubuwan dake faruwa ayanzu.

A  wata budaddiyar wasikar da ya rubuta, Ahmad wanda dan asalin jihar Adamawa ne yace lokaci yayi da yan boko zasu soma tunanin auren mace fiye da daya.

Shi dai dan fafutukar tuni ya kara .

Ga wasikar kamar haka:

Assalamu alaikum Jama’a. Barkanmu da sake saduwa a wannan dandalin. Allah yayi mana jagora. Amin.

Ranan Juma’a, 20/11/2020, a gidan marigayi Senator Buba Lamu, a Kolere Mini, aka daura min aure da Hajiya Maryam Buba Lamu. Muna masu godiya da dinbin gaisuwa da fatan alheri da kuka tura mana ta wannan dandali da kuma ta waya. Allah ya bar zumunci. Allah ya saka muku da mafificin Alherinsa. Amin.

Ga masu hali, qara aure ya zama wajibi, musamman idan kai dan Arewa ne. Allah zai yaye mana masifu da yawa, da sukke addabanmu. Wannan shine Jihadin. Iyali itace ginshikin al’umma. Idan kana da halin yi, toh amma kana taqama wai kai dan boko ne, saboda haka ba zaka qara aure ba, toh Wallahi bokonka na banza ne, baiyi tasiri ba. Allah yasa mu gane. Amin.

Yahudu da Nasara sun lashi takobi sai sun ga bayanmu. Suna yi mana yaqin sunquru irin na qare dangi, ta hannun Boko Haram, kidnappers, armed robbers, da sauran ta’addanci. Ta hanyan rushe addininmu da al’adunmu kuma, suna amfani da tashan television na Arewa 24, su gidan Radio Dandal Kura, da ire irensu.

Ya jama’a, a Arewa muna da mata da yawa, masu nagarta, kuma masu son zaman aure, toh ammah kash, babu maza masu zuciyan yin auren. Yawanci mazaje masu halin qara aure suna tsoron matansu, domin gudun abinda zai biyo baya! Allah wadan naka ya lalace!

Ina yiwa mazajenmu masu hali nasiha, don Allah don Annabi, mu qara aure, domin taimakawa wajen ceton al’umma. Ku kuma mata, kuji tsoron Allah ku bar mazajenku su qara aure. Wannan shine jihadin. Ya Allah ka sa mufi karfin zukatanmu. Amin.

Ya Allah kayi mana jagora a kan wannan kudurin na ceton al’umma. Ya Allah ka ceci Arewa daga sharri da makircin Yahudu da Nasara. Amin ya Hayyu ya Kayyum.

Dr. Idris Ahmed.
24/11/2020.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

NISHADI

Maganar Ladin Sima gaskiya ne – Naziru Sarkin Waƙa

Published

on

Maganar Ladin Sima gaskiya ne – Naziru Sarkin Waƙa

Naziru serkin waƙa, ya gaskata Ladin Sima, a kan batun rashin biyan masu fitowa a film yadda ya kamata.

Sarkin Waƙa ya ƙalubanci su Falalu da Ali Nuhi da su fito suyi rantsuwar ƙaryata batun idan ƙarya aka musu, inji shi.

Bayanan hakan ya sako su ne a shafinsa na facebook cikin Bidiyo mai tsawon mini 6 da daƙiƙu 45.

Tirka-tirkan ya samo asali ne bayan hira da BBC Hausa ta yi da Ladin Sima a cikin shirinta na Daga Bakin Mai Ita, inda ta bayyana cewa a duk finafinai da ta fita ba’a taɓa biyanta naira dubu 40 ko 50 ba, hasali ma tace a ranar da suka gudanar da tattaunawar ma ta je ɗaukar Film naira dubu 2 aka biyata.

Continue Reading

NISHADI

Ranar Bikin Farar Kaza su Balbela ba sai angayyace suba. Hajiya Zainab Abdurrahman Mai Agogo

Published

on

A madadin ɗaukacin ma’aikatan kamfanin Binkola Communication Services, da Shafin Voice of Arewa VOA, muna  taya shugabar  kamfanin ta WhiteBlood Multimedia Services, kamfanin da ke da mallakin shafin Kakaki Hausa da Farin Jini TV, Hajiya Zainab Abdurrahman Mai Agogo murnar zagayowar ranar haihuwarta a wannan rana ta 8 ga watan Yunin shekarar 2021.

Zainab Abdurrahman Mai Agogo fitacciyar yar jarida ce a jihar Kano da ta yi aiki a gidajen rediyo daban – daban da ke Kano, kuma tana cikin mata ƙalilan da su ka samu gogewa dai-dai da zamani a harkar yaɗa labarai, wanda hakan ne ya ba ta karfin gwiwar buɗe kamfanin WhiteBlood Multimedia Services.

Haƙiƙa Zainab Abdurrahman Mai Agogo tana daga cikin ƴan jarida mata a jihar Kano da ma arewacin Najeriya da su ka karɓi chanji a harkokin yaɗa labarai tare da komawa duniyar Intanet wajen yaɗa labarai da sauran shirye-shirye

A bisa haka muna addu’ar Allah ya sanya albarka a shekarun da suka gabata, da kuma Shekarun da za ki yi a nan gaba.

Continue Reading

NISHADI

Ranar Waƙa Ta Duniya: Wani Mawaƙi Ne a ranku?

Published

on

Daga Kakaki Hausa.

Ranar 21 ga watan Maris ɗin kowacce shekara rana ce da Majalisar dinkin Duniya ta ware domin jaddada muihimmancin rubutacciyar waka ga al’ummar duniya gaba daya dangane da ilimantarwa da fadakarwa da kuma samar da nishadi.

Rubutacciyar wakar, kamar yadda majalisar ta ce, hanya ce da ke bayyana halayen al’umma da al’adunsu da fasaharsu. Haka kuma wani tsari ne na samar da kaifafa tunani da natsuwar ruhin dan Adam, don haka ne ma majalisar ta ware rana ta musamman domin tunawa da ita.

An tabbatar da ranar 21 ga Maris ce a matsayin ranar Bikin Rubutattun Wakoki ta Duniya a yayin taron kungiyar Bunkasa Ilimi ta Majalisar dinkin Duniya (UNESCO), karo na 30 da ya gudana a birnin Paris, kasar Faransa, a shekarar 1999.

Continue Reading

BABBAN LABARI

Copyright © 2020 VOA voiceofarewa.ng