TARO KARO NA 17 MAI TAKEN MASU TA’ANNATI DA KAFAFEN YAƊA LABARAI NA ZAMI MAI ALAƘA DA FARAR HULA DA SOJI
Taron ƙarawa juna sani na kwana ɗaya da haɗin gwiwar Rundunar Sojoji ta ƙasa ɓangaren masu hulɗa da farar Hula, tareda ƙungiyar Security Affairs Limited, wanda aka gudanar a ranar Laraba 25/01/22 a Otal din City Green dake ƴola jahar Adamawa.
Jigon Taron shine: Imperatives of Non-kinetic line of Operations in Asymmetric Warfare, wand babban hafsan soji mai hulɗa da jama’a na sojan Najeriya Manjo Janar MG Kangye ne ya jagoranci taron ƙarawa juna sanin.
A cikin jawabinsa, Kangye ya jaddada bukatar samar da kyakykyawan alaƙa tsakanin farar hula da Sojoji wajen tunkarar makiyinmu ɗaya, wato rashin tsaro.
A yayin ƙaddamar da takarda ta ɗaya wanda Maj. Gen. Eap. Undiandeye, psc plsc fdc ICTF DSS MASSS Msc fcm Fcai, Director Psychological Warfare Defense Headquarters, ya ƙaddamar ya nuna bukatar ƴan Jaridu, ƙugiyoyin siyasa da sauran masu ta’ammali da kafafen yaɗa labarai na zamani (social media) su kasance masu tantance labari dakuma sanin sahihacin labari kafin yaɗawa.
Sannan ya nuna irin illa da ka iya faruwa idan har aka yi amfani da kafofin ba bisa yadda ya dace ba, yace “ko wannan zanga-zangar ta neman kawar da rundunar SARS wadda ta jawo babbar naƙaso ga Najeriya ma ta (Social Media) aka somata, sabida haka mu zamo masu haƙuri da amfani da kafafen yadda ya kamata cikin ili.”
Mai gabatar da takarda na biyu Dokta Lanre Adebayo ya bayyana irin rawar da kafafen sadarwar zamani ke takawa, wadda suka haɗa da samar da zaman lafiya da kuma kare martabar Najeriya ta hanyar baiwa Jami’an tsaro sahihan bayanan da ake buƙata, musamman na Sojoji.
Yakuma ce “Sojoji da ƴan Jaridu su kasance masu haƙuri da juna domin samar da mafita ga ƙasar, sabida abinda ka shuka shi zaka girɓa.”
Taron ya samu halartar Masu Ta’ammali da kafafen yaɗa labarai na zamani (Social Media) da ƴan Jaridu da Sarakunan Gargajiya da Ƙungiyoyin fararen hula dadai sauransu.
Kanwa uwar gami wanda shine Ummul’abaisa na gudanar taron, Amb. Austin Peacemaker shugaban ƙungiyar Security Affairs Limited, shi ya kasance mutum na ƙarshe da yayi jawabi, inda ya godewa mahalarta taron da nuna buƙatar al’umma su zamu masu kishin ƙasa.
A ƙarshe, an karrama mahalarta taron da takardar shaidar halarta, da wata ihsani domin rakiya.
Recent Comments