Da Ɗumi Ɗuminta: Aliyu Muhammad Tukur Binkola shine sabon mai magana da yawun Shugaban ƙungiyar Maharba ta ƙasa
A yau Jumma’a 14 ga watan Janairu Mai girma Shugaban ƙungiyar Maharba ta ƙasa ya amince da naɗa Aliyu Muhammad Tukur Binkola a matsayin mai magana da yuwunshi kan abinda ya shafi sha’anin ayyukan Maharba dake Nigeria baki ɗaya.
Baba Tola ya naɗa Aliyu Binkola ne dan maye gurbin marigayi Ibrahim Abdul-Aziz na Muryar Amurka wanda ke da wannan matsayin a lokacin da yake raye.
Baya ga ƙarin jajanta wa iyalan Marigayin ya kuma sake amincewa da baiwa Aliyu Muhammad Tukur Binkola wannan matsayi na mai magana da Nyawunshi wato Cheif Press Sacatary Kenan a turance.
Aliyu Muhammad ya zama mai magana da Nyawun Shugaban ne bayaga irin rawar da yake takawa a kan ayyuka na sha’anin yaɗa labarai, wanda a yanzu haka shine wakilin gidan Talabijin na Farin Wata TV, a jahohinnan biyu wato Adamawa da Taraba da kuma Vision FM Nigeria har’ila yau dai shina mai mallakar kafar dake yaɗa labaranta a kan yanar gizo wato Voice of Arewa VOA mai adireshin www.voiceofarewa.ng
Aliyu dai yayi ayyuka a kafen yaɗa labarai da dama a jahar Adamawa da wasu jahohi na Arewacin Nigeriya wanda har yanzu kuwa yana kan wannan aikin.
Har zuwa yanzu da Allah ya bashi damar zama mai magana da Nyawun Shugaban ƙungiyar maharba ta ƙasa Alh. Muhammadu Usman Tola (Baba Tola).
To saidai wannan muƙamin na zuwa ne a daidai lokacinda ake fama da matsala kan harkokin tsaro a faɗin ƙasar bakiɗaya wadda kuwa jami’an tsaro na yin haɗin guiwa da ƴan sa kai ta maharba dan kawo ƙarshen waɗannan fitintinun.
Wannan na zama tambaya ta farko da wakilin mu ya yiwa sabon mai Magana da yawun Shugaban ƙungiyar maharban.
To sai da Aliyu yace “wannan shine babban abun da zasu maida hankali akai kasancewar tsaro dai ta kowace amma tun da Allah ya basu hakkin taimakawa al’umma za suyi duk wata mai yiwuwa wajen ganin sun sauƙe nauyin da Allah ya ɗora musu.
“kuma akwai buƙatar Gwamanti ta ƙara mai da hankali kan waɗannan ƴan sa kai ta Maharba da ta Amin ce su taimakawa harkokin tsaro a ƙasar, sannan Gwamantin ta ƙara dubasu da kayan aiki da kuma abinda za’a sarrafa rayuwa da ita.
“Kuma muna ƙara kira ga maharba da su san cewa duk abinda za suyi kada su kuskura su ɗauki doka a hannun kuma su guji shiga abinda bai shafesu ba, domin mu Maharba Mutane ne masu ɗa’a da kuma bin doka da oda.
“kuma muna ƙira ga maharba idan akwai abinda ya shige musu duhu to kada suyi aiki cikin duhu su tuntuɓi shuwagabanninsu don warware matsalar.
“ Sannan muna kira da Kwamishinan ƴan sanda na jahar Adamawa akwai Maharba kusan tara da jami’an tsaro suka kama bisa zarginsu da aikata wasu laifuka, muna roƙon a tsananta bincike da kuma adalci a kansu tareda hukuntasu kamar yadda dokar ƙasa ta bada umarni”.
Daga bisani Sabon mai magana da Nyawun shugaban Maharban Najeriyan Aliyu Muhammad Tukur Binkola, ya yi fatan Allah ya ƙara wa Najeriya zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Recent Comments