Tun bayan ficewa daga Nigeria zuwa hutu a ƙasar Amurka da Salihu Tanko Yakasai yayi, wasu kalamai mabanbanta na ta fitowa akan wannan Tsoho hadimin Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Gandauje
Kalaman da ke nuni da cewa ya ƙaura a Najeriya Wanda wasu daga ciki jaridu na Shafukan sada zumunta, suka wallafa labarin
Saidai Salihu Tanko Yakasai ya musan ta wannan proparganda da akayi ta haɗawa wanda yanzu haka ma ya wallafa labarin kammala hutunsa a ƙasar Amurka, kuma tuni yana kan hanyar zuwa gida wato Kano a Najeriya

Salisu Tanko Yakasai da wallafa hakan bayan awa ɗaya daya wuce a shafinsa na facebook yana cewa
“Alhamdulilah na kammala hutu na a kasar America kuma ina kan hanya ta ta komawa Kano tumbin giwa, ko da mey ka zo mun fi ka, duk dadin turai bata kai gida kwanciyar hankali ba. Ka sakata ka wala sai a gida, ka ci gurasa da masa, ka ci tuwo da man shanu, ka sha koko da kosai. Ka ji kiran sallah ta ko ina, ka ga yan’uwa da abokan arziki. Fatan mu shi ne, Allah sa Kano da arewa da Najeriya ta samu ci gaba da duk wani abun da yake ba mu shaawa a turai, da sauran kasashen da suka ci gaba, muma mu same shi a nan. Da yardar Allah, wannan lokaci zai zo, ko ba’a zamanin mu ba, toh a zamanin ‘ya’yan mu da jikokin mu in sha Allah. Amin Ya Rahman. 👏

Salihu Tanko Yakasai (Dawisu)
Masoyin Kano da Arewa da Najeriya.
Recent Comments