A madadin ɗaukacin ma’aikatan kamfanin Binkola Communication Services, da Shafin Voice of Arewa VOA, muna taya shugabar kamfanin ta WhiteBlood Multimedia Services, kamfanin da ke da mallakin shafin Kakaki Hausa da Farin Jini TV, Hajiya Zainab Abdurrahman Mai Agogo murnar zagayowar ranar haihuwarta a wannan rana ta 8 ga watan Yunin shekarar 2021.
Zainab Abdurrahman Mai Agogo fitacciyar yar jarida ce a jihar Kano da ta yi aiki a gidajen rediyo daban – daban da ke Kano, kuma tana cikin mata ƙalilan da su ka samu gogewa dai-dai da zamani a harkar yaɗa labarai, wanda hakan ne ya ba ta karfin gwiwar buɗe kamfanin WhiteBlood Multimedia Services.
Haƙiƙa Zainab Abdurrahman Mai Agogo tana daga cikin ƴan jarida mata a jihar Kano da ma arewacin Najeriya da su ka karɓi chanji a harkokin yaɗa labarai tare da komawa duniyar Intanet wajen yaɗa labarai da sauran shirye-shirye
A bisa haka muna addu’ar Allah ya sanya albarka a shekarun da suka gabata, da kuma Shekarun da za ki yi a nan gaba.
Recent Comments