Connect with us

KASUWANCI DA SANA'A

Kamfanin NNPC ya koma hannun ƴan kasuwa – Buhari

Published

on

Kamfanin NNPC ya koma hannun ƴan kasuwa – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin mai na kasar wanda aka sauya wa fasali, inda a yanzu kamfanin na NNPC ya koma wani kamfanin kasuwanci mai zaman kansa

An yi kaddamarwar ne a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a Abuja babban birnin kasar ranar Talata.

Shugaba Buhari ya fara ne da gode wa mahartar taron, wanda ya kira shi da ”mai dimbin tarihi”.

A jawabin da ya gabatar a wurin taron, Shugaba Buhari ya ce an mayar da ikon gudanar da kamfanin ga ‘yan kasuwa ne, saboda inganta shi, don samar wa kasar makashin da take bukata.

Ya kuma kara da cewa ”daga yanzu kamfanin NNPC ya koma karkashin gudanarwar ‘yan kasuwa, zai kasance kamfani mai zaman kansa ta yadda zai yi gogayya da takwarorinsa a fadin duniya, domin ci gaba da bunkasa hannayen jari sama da miliyan 200 tare da habaka fannin makashi a fadin duniya”.

”A yanzu doka ta dora wa kamfanin alhakin tabbatar da samar wa Najeriya wadataccen makashin da take bukata domin samun habakar tattalin arzikin ta hanyar farfado da wasu fannonin da ke bukatar makashin,” in ji Shugaban na Najeriya.

Sabuwar alama ta kamfanin NNPC

An kuma sauya wa Kamfanin nan NNPC alama.

KASUWANCI DA SANA'A

Kano: Coca-cola Ya Maka Pop-Cola Agaban Kotu

Published

on

Kano: Coca-cola Ya Maka Pop-Cola Agaban Kotu

Kamfanin Coca-Cola ya gurfanar da kamfanin Mamuda Beverages, masu yin Lemun Pop-cola a gaban Kotun ɗaukaka ƙara da ke Kano, bisa zargin satar fasaha.

Lemon Pop-cola dai kamfanin Mamuda Beverages ne ya ƙaddamar a cikin watan Yunin shekarar nan.

Tun da farko kwafin ƙarar da kamfanin na Coca-Cola ya gabatar wa kotun, ya yi ƙorafin yadda kamfanin Mamuda Beverages ya saci fasahar zanen da ke jikin kwalbar Coca-Cola, da a turance ake kira da RIBBON ya yi matuƙar kama da wanda ya ke jikin Coca-Cola, tare kuma da kwaikwayon sunan na Coca-Cola inda aka fitar da Pop-cola.

Haka kuma kamfanin na Coca-Cola ya sanar wa kotun cewa shi ke da haƙƙin mallakar sunansa tareda zanen na RIBBON a ciki da wajen Najeriya.

Kamfanin ya ƙara da cewa waɗannan siffofi mallakin kuma sun yi amfani da su a kasashen duniya daban-daban ciki har da Najeriya.

Hakazalika kamfanin na Coca-Cola ya buƙaci kotun da ta haramtawa kamfanin Pop-cola yin amfani da wadannan siffofi a manyam allunan talla da motocin da ke sufurin lemon Pop-cola, sakamakon yin amfani da siffofin da ba hakkin mallakarsa ba ne.

A nasa ɓangaren lauyan da ke kare kamfanin Mamuda Beverages, George Ogunyomi, ya buƙaci kotun da ta ba shi lokaci domin yin martani ga wannan ƙorafin satar fasaha da kamfanin ya yi musu.

A ƙarshe mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 11 ga watan Disamban 2021

Continue Reading

KASUWANCI DA SANA'A

FAO Ta Tallafa wa Manoma da Masu Ƙaramin Ƙarfi a Adamawa

Published

on

Kwamishinan ayyukan noma na jahar Adamawa, Alhaji Umaru Iya Daware. ya ƙaddamar da tallafi na kayan noma wanda Hukumar bunƙasa abinci wato Food Agricultural Organization FAO ta gudanar, ta tallafawa manoma maza da Mata musamman masu ƙaramin ƙarfi da wandda basu da maza.

Wannan tallafin ya gudana ne a ƙofar hakimin Ribaɗu Alh. Abubakar Aliyu Mahmud, inda kwamishinan ya gode wa hukumar bunƙasa abinci, da namijin ƙoƙari da suke yi don kawarda yunwa a jahar Adamawa, yace wannan tallafin yazo ne a lokacinda shi mai girma gwamnan jahar Adamawa Rt Ahmadu Umaru Fintiri yake tallafawa ƴan jahar Adamawa domin kawar da yunwa.

Ya ƙirayi manoma da suyi aiki da abinda aka tallafa musu don ganin sun mori wannan kayakinda aka kawo musu, cikin abinda aka kawo sun hada da Irin Masara, Irin Kuɓewa, Taki da sauransu.

A jawabinsa Dakta Abdullahi Abubakar Usman, Kodineta na Hukumar bunƙasa abinci na Jahar Adamawa yace kasar Canada ta tallafawa manoma domin kawar da yinwa dakuma bunƙasa noma a jahar Adamawa dama Ƙasa baki-daya, yana ƙira ga manoma dasuyi amfani da wannan kayakin da aka basu musamman mata wa’anda aka basu iri na Kuɓewa wato kid wan, don moriyan wannan tallafin.

Anashi jawabin shugaban ƙaramar Hukumar Fufore Alh Musa Umaru Jauro Gurin, ya godewa Hukumar bunƙasa abinci ta kasar Canada da sanya karamar Hukumar Fufore a ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi na jahar Adamawa da zasu mori wannan tallafin, yace “in Allah ya yerda Al’umman ƙaramar Hukumar Fufore zasuyi aiki da wannan tallafin kamar yadda yakamata. Kuma wani lokaci zamu tallafawa wata kasa da abinci kamar yadda ake tallafamana”.

Ardo Ribaɗu Alh Abubakar Aliyu Mahmud, a jawabinsa shima yagodewa Hukumar bunkasa abinci ta kasar Canada da jami’anta dana mijin kokarinda sukeye wojen tallafawa karamar Hukumar Fufore, acewarsa “wannan karo na Uku ne tun yagaji mahaifinsa a wannan masarautan suke tallafawa manoman mu” basaraken ya ƙirayi al-ummansa dasu haɓaka wojen aiki da wannan kayakin, ya ƙara da cewa Hukumar wojen tallafin bata nuna banbancin addini ko ƙabilanci ba, yakuma gode wa mai girma gwamnan jahar Adamawa Rt Hon Ahmadu Umaru Fintiri da haɗin kai da yake baiwa wannan hukkuman bunkasa abinci, yakirayi wa’anda suka amfana da suyiwa Allah kar su sayarda abinda aka basu.

Daya daga cikin wa’anda suka amfana da wannan kayakin tallafin Mr Raymond, ya godewa Hukumar bunkasa abinci ta kasar Canada da tallafa musu da sukayi, musamman su manoma na ƙaramar Hukumar Fufore, yace bazasuyi Ƙasa a Guiwa ba wojen aiki da wannan kayakin da aka raba musu.

Continue Reading

KASUWANCI DA SANA'A

Ƴan sanda na matsa-kaimi wajen yaƙar masu sayar da magungunan amfanin gona na bogi

Published

on

-An dawo da katon 36 na kayan amfanin gona (Chemicals) na jabu game da Naira Miliyan Ɗaya

Ziyarce mu a Facebook Voice of Arewa VOA latsa nan

Jami’an rundunar ƴan sanda da ke aiki a hedikwatar ƴan sanda reshen ƙaramar hukumar Jada da ke aiki tareda haɗin gwiwar cibiyar yaƙi da jabun hanyoyin don wayar da kan jama’a da kuma hana yaɗuwar magungunan na bogi a cikin jihar.

Waɗanda ake zargin sun buya ne don gudun kada a kama su inda suka ce za su tashi daga wata Kasuwar zuwa wata kasuwar musamman a ƙauyukan Jada, Ganye da Toungo, suna sayar wa tareda damfarar Manoma da ƴan kasuwa.

Kwamishinan ƴan sanda Aliyu Adamu Alhaji, psc, ya tura jami’ai na rundunar don bayyana wani kamfen da aka yi wa lakabi da “Kawar da laifi da mai laifi da kuma kama kungiyar bayan rahoton da aka samu daga Anti-counterfeit Network (A C N).

Bincike ya zuwa yanzu ya nuna cewa waɗanda ake zargin suna rabar da jabun maganin na Agro-Chemicals ga Kananan Manoma tun a farkon Mayu, 2021 a halin yanzu, a wani ɓangare na ƙoƙarin daƙile ayyukan zamba da sauran laifuka masu nasaba da hakan a jihar, Kwamandan da ke aiki cikin haɗa kai don zurfafa bayanan sirri da karfafa tsaro, ya ba da umarnin a gano waɗanda ake zargin, a kamo su, a bincike su sannan a gurfanar da su a gaban Kotu bayan sun kammala bincike.

Hakanan rundunar ta yi kira ga jama’a, musamman Manoma da ƴan kasuwa da su kula sosai da sayan magungunan kashe kwari, da kai rahoto ga ofishin ƴan sanda da ke kusa da yankin da suke zaune.

Sa hannu: DSP SULEIMAN YAHAYA NGUROJE, ANIPR, JAMI’I MAI HULƊA DA JAMA’A NA RUNDUNAR ‘YAN SANDA NA JAHAR ADAMAWA 08065604764

Continue Reading

BABBAN LABARI

Copyright © 2020 VOA voiceofarewa.ng