Connect with us

BABBAN LABARI

Kotun Ƙolin Amurka ta soke ƴancin da mata suke da shi na zubar da ciki

Published

on

Miliyoyin mata a Amurka za su rasa damar da suke da ita ta zubar da ciki, bayan Kotun Kolin kasar ta yi watsi da dokar shekaru 50 da suka gaba ta Roe v Wade.

Hukuncin dai zai share hanya ga jihohin kasar na haramta zubar da ciki a hukumance.

Ana ganin yawancin jihohin za su fitar da sabbin dokoki kan zub da cikin. Tuni 13 daga ciki suka gabatar da kudurin haram zub da cikin.

Shugaba Joe Biden ya bayyana matakin da mai ta da hankali, tare da bukatar jihohi su sake duba lamarin.

Bayan hukuncin na Kotun Kolin, ana sa ran za a samu raguwar yawan masu zub da cikin, sannan mata miliyan 36 ka iya daukar ciki, kamar yadda binciken wata cibiya mai suna Planned Parenthood wadda ke fafutukar taimaka matan da ke son zub da ciki ya bayyana.

Masu zanga-zanga daga dukkan bangarorin biyu sun cika wajen kotun, yayin da ‘yan sanda ke kokarin tabbatar da doka da oda.

Wata mai fafutuka da ba ta goyon bayan zub da ciki, ta shaida wa BBC tana cike da farin ciki, da matakin da kotu ta dauka. “Ba wai kawai an yi doka ba ne, dokar da hukuncin na nufin bai wa wani ‘yancin rayuwa,” in ji ta.

Sai dai an samu rabuwar kauna, wasu na maraba da hukuncin, yayin da wasu ke bakin ciki da hakan.

Wakiliyar BBC, Samantha Granville, ta rawaito daga asibitin zub da ciki da ke Little Rock, a Arkansas, cewa ana wallafa hukuncin kotun, nan take aka rufewa marasa lafiya kofa yayin da take jin koke-koken mata daga dakuna kafin daga bisani a umarce ta da barin asibitin. Wannan dai daya ce daga cikin jihohin da suke maraba da hukuncin.

Masu goyon bayan hukuncin kotu na haramta zubda ciki na farin ciki da hakan

Nasarar da aka yi kan dokar ta shekarar 1973 Roe v Wade, da Kotun Koli ta yi watsi da shi, da cewa mata na damar zubar da ciki karkashin kundin tsarin mulkin Amirka.

A karkashin wancan hukuncin zai bai wa matan Afirka cikakkiyar damar zub da cikin da bai wuce watanni uku ba.

A wannan karon Kotun Kolin ta duba shari’ar Dobbs v Jackson na kungiyar kula da lafiyar mata, da suka kalubalanci haramcin da Mississippi ta yanke na zub da cikin da ya haura makwanni 15. Alkalai biyar ne suka amince da hukuncin da suka hada: Samuel Alito, Clarence Thomas, Neil Gorsuch, Brett Kavanaugh da Amy Coney Barrett.

Alkalin-alkalai John Roberts ya rubutu na shi ra’ayin na kashin kai, cewa ya yin da ya ke goyon bayan hukuncin haramcin da Mississippi ta yi, ba zai kara cewa komai ba.

Alkalai uku da ba su amince da matakin sauran ba – Stephen Breyer, Sonia Sotomayor da Elena Kagan – sun rubuta cewa sun tsaya kan bakarsu ne, kuma sun yi bakin ciki da hukuncin kotun da zai shafi rayuwar miliyoyin matan Amirka, wadanda dama can sun rasa ikon zub da ciki karkashin kundin tsarin mulki.

Hukuncin kotun na ranar Juma’a ya sauya abubuwa da dama musamman kan batun zub da cikin, alamu sun nuna za a samu rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan siyasa.

A jihohin da batun zubda cikin ke matakin ba-yabo-ba-fallasa, kamar Pennsylvania, Michigan da Wisconsin – za a iya gabatar da shi a lokutan zabe. Ya yin da ga wasu jihohin kuma, hukuncin zai bude sabon babi na mutane ka iya ficewa daga jihar su tafi wata domin zubda ciki kuma hukunci ba zai hau kansu ba.

Lokacin da ya ke nuna rashin jin dadi kan hukuncin kotun, shugaba Biden ya shaidawa matan jihohin da aka haramta zubda cikin su tfi wata jihar domin samun biyan bukata.

Gwamnonin jam’iyyar Democratic a jihohi kamar California, New Mexico da Michigan tuni suka sanar da shirinsu na tabbatar da bai wa mata ‘yancin zubda ciki karkashin kundin tsarin mulkinsu.

Gwamnan jihar Mississippi Tate Reeves ya yi maraba da hukuncin, ya kara da cewa jiharsa za ta ja ragamar kawo karshen wani abu da ya dade ya na ci wa mutane tuwo a kwarya a tarihin Amirka.

“Wannan mataki zai zamo silar bugun zuciyar sabbin haihuwa, karin sayan kayan wasan yara, da katin shaidar cin jarabawa a makarantu, samar da karin kungiyoyin kwallon kafa na matasan gobe. Wannan lokaci ne mai cike da annushuwa da farin ciki!” kamar yadda ta rubuta.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

BABBAN LABARI

Anbaliya ya tafi da mutum biyu kuma gidaje sama da dari biyu sun rushe a loko dake karamar hukumar song na jihar Adamawa 

Published

on

By

Daga lado salisu Muhammad garba 

Wani matashi wanda Anbaliya ya shafa mai suna Rabiu isiyaku ya shaidawa manema labarai chewa gidaje da shagunan su Akasuwa basu sa yawan asarar da sukayi ba

Akasuwan buhuna kuma Abinchi fiye da buhuna dari uku da hamsin ne suka lalace inji Alhaji ibirahim Alliru shugaban masu sana’ar sai da hasti na karamar hukumar song 

Alhaji musa isa magidanchine a kauyen loko inda abin yafaru yace gidajen su gaba daya ruwa ya rusa basuda ma inda zasu koma sai dai kan kwalta shima don ruwan bai tafi dashibane

Shugaban karamar hukumar song hon gidado Abdulsalam zasu yi mai yiwuwa kan wannan batun na Anbaliya don a halinyanzu mazauna yankin na cikin wani mawuyachin hali sakamakon wanan Anbaliyan da yafaru 

Continue Reading

BABBAN LABARI

Babban Sufeton ‘Yan-sandan Najeriya ya haramta amfani da lambar mota ta musamman ta tsaro Usman Alkali Bab

Published

on

By

Shugaban ‘yan-sandan ya bayar da umarnin kwace lambar a ko’ina a NajeriyaImage caption: Shugaban ‘yan-sandan ya bayar da umarnin kwace lambar a ko’ina a Najeriya
Babban Sufeton ‘yan-sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin hana amfani da lambar mota ta musamman ta tsaro wadda ake wa lakabi da SPY, a duk fadin kasar.

Umarnin ya biyo bayan irin matakan da shugaban ‘yan-sandan ke dauka na inganta tsaro da dakatar da yadda daidaikun mutane ke fakewa da wannan lambar mota su rika keta dokokin amfani da titi da sauran ka’idoji, kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga kakakin rundunar na kasa CSP Olumuyiwa Adejobi ta bayyana.

Sanarwar ta ce daga yanzu an haramta wa duk wata mota amfani da irin wannan lamba a ko’ina a fadin Najeriya.

Tare da umartar kwamishinonin ‘yan-sanda na jihohin kasar 36 da Abuja, da mataimakan sufeto janar na ‘yan sanda da su tabbatar da bin umarnin.

Shugaban ‘yan-sandan ya kuma umarci duk ‘yan-sanda da sauran jami’an tsaro da ke aiki da manyan mutane masu amfani da motocin da ke da irin wannan lamba, su tabbatar da bin umarnin ko kuma su fuskanci hadarin kamasu kan kin bin umarnin.

Dokar ta bukaci a kwace dukkanin irin wannan lamba a ko’ina a kasar.

Continue Reading

BABBAN LABARI

Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Nasarawa a majalisar wakilai ta kasa, Hon. Nassir Ali Ahmed ya taya al’ummar jihar Kano murnar bikin Sallah Babba.

Published

on

By

A wata sanarwa da dan majalisar tarayya ya fitar a ranar Lahadin, ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da lokacin bikin Sallah wajen yin addu’ar samun zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

Hon. Nassir Ali Ahmed ya tabbatar wa al’ummar mazabar sa cewa nasarorin da ya samu a wakilcin da yake yi musu ya same su ne bisak jajircewar sa wajen ganin sun samu wakilcin da ya dace a zauren majalisar.

Ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su kiyaye kyawawan dabi’un Musulunci wanda ya ya koya wa mabiyansa ta yadda za su zauna lafiya ba kawai da ‘yan uwa musulmi ba, har ma mabiya sauran addinai.

Hon Nassir Ali Ahmed ya kara da cewa, ba za a iya samun zaman lafiya da hadin kai a Najeriya ba, in ba tare da hakuri a tsakanin mabiya manyan addinai biyu na Musulunci da Kirista ba.

Bugu da kari, ya bukaci al’ummar musulmi da su rika nuna kauna da taimakawa ga makwabtansu da sauran jama’a, yayin da suke gudanar da bukukuwa irin wadannan masu muhimmanci a rayuwarsu.

Ahmed ya kuma yi fatan wannan lokaci na Sallah ya zama silar samun albarka, zaman lafiya, wadata da aminci ga ‘yan Nijeriya ganin cewa idan aka yi addu’a a wadannan kwanaki kalubalen da kasar nan ke fuskanta za su zama tarihi.

Continue Reading

BABBAN LABARI

Copyright © 2020 VOA voiceofarewa.ng