Connect with us

SIYASA

Najeriya ta fi gyaruwa a yanzu fiye da yadda na same ta – Buhari

Published

on

Duk da tsananin munin rashin tsaro a faɗin ƙasar nan, kashe-kashe barkatai da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa “za ta bar Najeriya a cikin ingantaccen yanayin da ya fi lokacin da gwamnatin muka gada nesa ba kusa ba.”

Buhari ya yi wannan cika-baki a cikin wata tattaunawar da ya yi wa jaridar Bloomberg ta hanyar amsa tambayoyin da su ka tura masa ta e-mel.

An tambayi Buhari ya yi bayanin Gwamnatin sa a kan abubuwa uku da ya yi kamfen zai kakkaɓe kafin ya hau mulki, wato rashawa da cin hanci, inganta tattalin arziki da kuma samar da tsaro.

“Za mu bar Najeriya cikin halin inganci fiye da lokacin da muka same ta nesa ba kusa ba.

“A yanzu cin hanci da wawurar dukiya duk an daina ɓoyewa idan an ga ana yi. Saboda ‘yan Najeriya sun samu damar fallasa masu wawurar dukiya, ba tare da jin tsoron fallasa su ba. Sannan kuma ana ƙwato kuɗaɗen da aka wawura.

“Batun tsaro kuma a yanzu ‘yan Boko Haram ba su riƙe da kowane yanki a Najeriya. An karkashe shugabannin su, kuma gagariman ayyukan inganta ƙasa da muka yi sun ɗora ƙasar nan bisa turbar ci gaban ƙasa mai ɗorewa.”

TAM: Ka karaɗe Najeriya ka na kamfen ɗin cewa idan aka zaɓe ka, za ka kawar da cin hanci da rashawa, za ta samar da ingantaccen tsaro, kuma za ka gyara tattalin arzikin ƙasa wanda a lokacin ka ce a durƙushe ya ke.

Shin ya za ka auna irin nasarorin da ka samu ne? Me ya sa matsalar tsaro ta yi maka wahalar magancewa?

BUHARI: “Za mu bar Najeriya cikin halin inganci fiye da lokacin da muka same ta nesa ba kusa ba.

“A yanzu cin hanci da wawurar dukiya duk an daina ɓoyewa idan an ga ana yi. Saboda ‘yan Najeriya sun samu damar fallasa masu wawurar dukiya, ba tare da jin tsoron fallasa su ba. Sannan kuma ana ƙwato kuɗaɗen da aka wawura.

“Batun tsaro kuma a yanzu ‘yan Boko Haram ba su riƙe da kowane yanki a Najeriya. An karkashe shugabannin su, kuma gagariman ayyukan inganta ƙasa da muka yi sun ɗora ƙasar nan bisa turbar ci gaban ƙasa mai ɗorewa.”

Batun Matsalar Tsaro: Cikin 2015 Boko Haram na riƙe da yankuna waɗanda faɗin su ya kai faɗin ƙasar Belgium. Amma a yan Boko Haram sun kusa ƙarewa ƙarƙaf a matsayin su na ƙungiya mai ƙarfin makamai.

An kashe shugaban ISWAP a wani farmaki da Sojojin Sama na Najeriya suka kai masa cikin watan Maris.

Jiragen yaƙin da muka sayo daga Amurka da kuma bayanan siriin da Birtaniya ke ba mu a yanzu, duk gwamnatin da muka gada ba ta samu waɗannan ba. Wannan kuma hujja ce mai nuna cewa tabbas manyan ƙasashen da mu ke hulɗa da su, sun fi gaskata ƙoƙarin gwamnatin mu har suka gina ƙaƙƙarfar alaƙar magance matsalar tsaro da wannan gwamnati, fiye da gwamnatin da muka gada.

Saboda haka mu na roƙon waɗannan manyan ƙasashe da mu ke hulɗa da su, su ayyana cewa ƙungiyar IPOB ta ‘yan ta’adda ce. Ko sisi ba za su kashe ba wajen ayyana IPOB ƙungiyar ta’addanci. Shugabannin IPOB su na samun mafaka a ƙasashen Turai ta Yamma, su na watsa shirye-shiryen su na radiyo daga can zuwa cikin Najeriya masu ɗauke da kalaman ƙiyayya tsakanin ɓangarorin Najeriya. Daga Landan su ke watsa shirye-shiryen zuwa cikin Najeriya.

Sannan kuma su na kashe miliyoyin daloli wajen roƙon ‘Yan Majalisar Amurka, su na kuma amfani da bankunan Turai da sauran hanyoyin hada-hadar kuɗaɗe na zamani su na sayo makaman da su ke bai wa mambobin su masu tayar da fitintinu a cikin Najeriya. Tilas sai fa an tsaida wannan.

Rikicin Makiyaya Da Manoma:

A tarihin Najeriya gwamnati na ce kaɗai wadda ta aiwatar da tsarin magance rikicin makiyaya da manoma, wanda mamayewar da aka yi wa dazuka da kuma yawaitar gina garuruwa ya haifar. Tsarin Tattara Kiwon Dabbobi Wuri Ɗaya ne kawai zai iya magance faɗace-faɗacen makiyaya da manoma. Duk da haka dai an rage tashe-tashen hankulan sosai, duk kuwa da cewa wasu gwamnoni sun ƙi goyon bayan shirin.

Batun Inganta Tattalin Arziki:

TAM: Wace nasara za ka ce ka samu wajen inganta tattalin arzikin Najeriya?

BUHARI: Manyan jaridun duniya irin su FT da Economist sun riƙa sukar Gwamnati na saboda yunƙurin da mu ka yi na daƙile dogaro da abinci daga waje, ta hanyar tashi mu dogara da noma abincin mu a cikin gida.

To yanzu ga shi nan yaƙin Ukraniya ya katse dukkan hanyoyin safarar abinci tsakanin ƙasashen duniya.

Mun shafe shekarun nan takwas mu na kashe maƙudan kuɗaɗe wajen gina titinan motoci, titinan jiragen ƙasa, inganta hanyoyin sufuriabu ne mai bunƙasa tattalin arziki a cikin al’umma. A fili ba a ganin sakamakon abin. Amma nan gaba kowa zai gane muhimmanci da albarkar da ke cikin sa.

Batun Yaƙi Da Cin Hanci Da Rashawa:

“Bari na fara da tsarin ƙarfafa masu tona asirin ɓarayin gwamnati, wato ‘whistleblowing’, wanda na shiga da shi a farkon zangon gwamnati na na farko. An samu nasara dawo da ɗaruruwan miliyoyin kuɗaɗe cikin Najeriya.

Ta hanyar yin aiki tare da ƙasashen waje da muke da kyakkyawan ƙawance, miliyoyin kuɗaɗen ƙasashen waje da aka dawo da su Najeriya daga Birtaniya, Amurka da Switzerland su na da yawa. Kuma daga cikin waɗannan kuɗaɗen ne aka riƙa raba wa marasa galihu kuɗaɗen tallafin korona a lokacin da korona ta ɓarke, ta tsayar da harkokin komai a duniya.

Kuma da irin kuɗaɗen ne aka riƙa gina manyan tituna, gadoji, titunan jiragen ƙasa da kuma ayyukan inganta wuta.

Ƙwato Kuɗaɗe Daga Hannun Ɓarayin Gwamnati:

Bari na buga maku misali. A daga Janairu zuwa Disamba 2021 kaɗai, an karɓo fiye da naira biliyan 152. An ƙwato dala miliyan 386, an ƙwato fiye da fam na Ingila miliyan 1.1, Yuro 157,000 aka ƙwato, kuma aka ƙwato Riyal na Saudiyya miliyan 1.7.

Ƙasashen waje sun ƙi amincewa su maido wa gwamnatin baya kuɗaɗen, saboda sun san sata-ta-saci-sata za su sake yi, su sake sace kuɗaɗen.

Amma da ya ke ƙasashen sun gaskata gwamnati na, sai su ka dawo mana da kuɗaɗen a yanzu.

Batun Tsadar Kayan Abinci:

TAM: Farashin kayan abinci ya nunka idan aka kwatanta da farkon hawan mulkin ka cikin 2015. Duk kuwa da ƙoƙarin da Gwamnatin ka ta yi, kuma ta ke kan yi wajen bunƙasa harkokin noma. Me ya sa gwamnatin ka ke fama da gaganiya kan ƙarin farashin abinci? Shin ko matsalar ƙarancin abinci na damun ka, idan aka yi la’akari da halin da ake ciki har a nahiyar ba ma a Najeriya kaɗai ba?

BUHARI: Ai da gwamnati na ba ta bijiro da shirin bunƙasa noma a cikin gida ba, da ba a san irin tsadar da kayan abinci za su yi ba a halin yanzu. Kuma idan aka duba, har yanzu ba mu kai ga noma wadataccen abincin da mu ke son a riƙa nomawa a cikin gida ba.

Tsare-tsare irin su Shirin Bayar da Lamuni Ga Manoma (Anchor Borrower’s) ya na tsimaka wa monoma su na rage yawan kwararowar abinci daga waje, musamman shinkafa.

Cikin 2021 an yi nasarar noma metrik tan miliyan 9 na shinkafa daga metrik tan miliyan 5.4 da aka noma cikin 2015.

Kai ko a lokacin fari da ƙarancin ruwa ma shinkafar da aka noma a wannan gwamnatin ta zarce wadda ake nomawa kafin 2015. Yanzu kusan an daina shigo da shinkafa daga waje. Lallai mu na samun ci gaba ta wannan fannin.

Matsalar Wutar Lantarki:

TAM: Shin ka na ganin gwamnatin ka ta magance matsalar makamashi kuwa? Idan akwai sauran abin da ba a yi ba, to mene ya kamata a yi ɗin?

BUHARI: Da farko dai mu na buƙatar ƙara himma sosai. Akwai ɗaruruwan ayyukan inganta wutar lantarki da ake kan yi a yanzu haka. Da yawan su akwai sa hannun manyan kamfanonin waje a ayyukan. Irin su Siemens AG na Jamus, domin ƙara bunƙasa wutar lantarki, ayyukan kuma sun kai zuba jarin dala biliyan 2.

Sannan kuma muna ƙoƙarin karkasa Babbar Tashar Wutar Lantarki zuwa yankuna, wato a samu ƙananan tashoshi daban-daban.

Aikin samar da wutar hasken sola na Nigeria Electrification Project ya ci dala miliyan 550, domin samar da sola ta SHS 20,000. Akwai kuma aikin sola ta ‘Hybrid’ ƙanana a wurare fiye 250.

Batun Matsalar Tallafin Fetur Da Yawan Ciwo Bashi:

TAM: IMF da Bankin Duniya da masana tattalin arziki da dama sun sha ba ka shawarar ka cire tallafin fetur. Me ya sa ka ƙi ɗaukar shawarar su?

BUHARI: To ai a yanzu haka ƙasashen Turai na Yamma da dama na amfani da tsarin biyan tallafin fetur (fuel subsidy). Abin da ya ci Doma ai ba ya barin Akwai!

Darasin da su ma Turawan Yamma ke koyo a zahiri a yanzu shi ne, wato wani tsarin a takarda kawai ya ke da tasiri. Amma idan aka yi amfani da shi, to al’umma ne masu ɗimbin yawa za su tagayyara.

Ai cikin 2021 gwamnati na ta tsara yadda za ta daina biyan tallafin mai a cikin wannan shekarar. Bayan shawara da masu ruwa da tsaki da kuma yanayin halin da ake ciki, sai mu ka ga cire talalfin fetur a yanzu ba abu ne mai yiwuwa ba.

Mu na ƙoƙarin bunƙasa hanyoyin tace mai a cikin gida, yayin da Matatar Ɗangote, Matatar BUA da Matatar Waltersmith su ka fara tace mai nan ba da daɗewa ba.

Batun yawan ciwo bashin da ake magana kuma, ai kun kasa fahimtar wani abu. Ai kuɗaɗen nan fa ayyukan cike giɓin wasu muhimman ayyukan da ba a yi ba ne a baya mu ke yi. Kuma a ko’ina cikin faɗin ƙasar nan ake yin ayyukan. Watsi da ayyukan inganta rayuwar jama’a da aka yi a baya ne fa ya jefa mu cikin matsalar tsaron da wannan gwamnati ta zo ta taras.

Mun gina titina sama da 800 na gwamnatin tarayya. Mu na kan aikin gyaran titina mai tsawon kilomita 650 na jiragen ƙasa.

Ta irin waɗannan ayyukan ne tattalin arzikin mu zai bunƙasa talallin arzikin mu

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SIYASA

Zaben Gwamna 2023: Zamu Kawo Chanji Idan Alumma Su Ka Bamu Dama- Salihu Tanko Yakasai

Published

on

By

Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PRP , Salihu Tanko Yakasai ya bayyana kudirorinsa na ganin Kano ta yi fice idan aka zabe shi babban zaben a shekara ta 2033.

A cewarsa, kudirorin nasa sun hada da yadda za a mayar da Kano ta zama cibiyar kasuwanci ba kawai a Najeriya ba, har da kasashen Afirka baki daya a cikin shekaru 10 masu har ta wuce jihar Legas.

Tanko Yakasai wanda ake yiwa lakabi da Dawisun Kano ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ya bar wasu aiyukan cigaba a bangarori bakwai, kamar; bunkasa Tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa, Inganta ilimi, lafiya da muhalli, sai inganta ma’aikatun gwamnati wato yadda za a gyara harkokin mulki gaba daya a jihar da kuma uwa uba inganta tsaro domin samun kwanciyar hankali da lumana.

“Ba wai kawai mun shiga Siyasa ido rufe bane,Muna da manufar bari wani abu da za’a dade ana tunawa dani, kuma hakan ba za ta samu ba sai idan mun mai da hankali wajen samar da ayyukan raya kasa, da kula da bukatun talakawa domin inganta rayuwar su su zamo abun kwatance a Cikin al’ummar Nigeria ” Inji Salihu Tanko Yakasai

Wadannan hanyoyi ne da muke ganin za mu iya gyara al’amuran Kano da kyau da kuma mayar da jihar zuwa mafi bunkasar tattalin arziki da wadata da za su ciyar da bangarori daban-daban na tattalin arzikin jihar gaba, kamar yadda na ambata wasu muhimman kudirori guda bakwai da Zamu mai da hankali akansu a matsayin manufofinmu”.

“Shirinmu cikakke ne kuma burinmu shine, ta yaya za mu sanya Kano ta zama cibiyar inganta kasuwanci ba kawai a Najeriya ba, har ma a Afirka a cikin shekaru 10, ta zarce Legas. Shi ya sa muka kiran shirinmu “Vision”. 2033″.

Tanko Yakasai, wanda yake da kwarin gwiwar lashe zaben ya bayyana cewa, “Abin farin ciki, muna wakiltar rukunin al’umma mai matukar muhimmanci a jihar Kano wato matasa kuma muna da tabbacin cewa su ke da kaso 70% na al’ummar kasar za su zabi wanda zai wakilce su, wanda ya san bukatunsu kuma yake cikisu .

Mun ji ra’ayoyin jama’a, kuma mun tabbata cewa mutane suna son ‘canji’ a jihar nan, sun gaji da halin da ake ciki, sun gaji da irin wadannan mutanen da suka shafe shekaru ashirin suna mulkarsu, kuma tabbas suna buƙatar canji”.

Salihu ya kuma yi alkawarin cewa idan ya zama gwamna, gwamnatin sa za ta zama gwamnatin matasa, wacce matasa zasu gudanar domin nuna cewa suma zasu iya jagorancin al’umma.

“Zai ba ku sha’awar sanin cewa shugaban sashin kowane bangare da na ambata a sama zai kasance wanda bai kai shekara 40 ba amma kwararre kuma mai matukar kishi wanda zai iya tsayawa ko ina a duniya kuma a girmama shi a matsayinsa na wanda yasan me yake.

Bugu da kari, dan takarar gwamnan na PRP ya yi kira ga matasa da su fito su karbi katin zabe na dindindin kuma su guji yin rijista sau biyu wanda zai hana su kada kuri’a a zabe mai zuwa.

Continue Reading

SIYASA

Hitaande Yalti Ummatoore Lesdi Nigeria

Published

on

By

Continue Reading

SIYASA

Saƙo da Ɗumi Ɗuminta Ga Ƴan Nigeria

Published

on

By

Prev1 of 2
Use your ← → (arrow) keys to browse
Prev1 of 2
Use your ← → (arrow) keys to browse

Continue Reading

BABBAN LABARI

Copyright © 2020 VOA voiceofarewa.ng