Connect with us

BABBAN LABARI

NOMAS Zasu Gudanar Da Taro Na Shekarar Ranar Litinin A Adamawa

Published

on

Kungiyar kafafen yada labarai ta Arewa maso Gabas, NOMAS zata gudanar da babban taronta na bana, a ranar Litinin, 2 ga Janairu, 2023 a Yola jihar Adamawa.

A cewar sanarwar da aka fitar ranar Juma’a, wanda sakataren riko na kungiyar, Malam Aliyu Muhammad Tukur Binkola ya fitar, “an shirya gudanar da babban taron da safe, 11 na safe, ranar Litinin, 2 ga watan Janairu, 2023, a dakin taro na Periscope Global Publishers. a saman bene na Arch Bello Ahmed Plaza, kan titin Lamiɗo Zubairu, Yola Town Bye-Pass, jihar Adamawa.

“Taron zai samu halartar shuwagabannin kafafen yaɗa labarai na yanar gizo da mawallafa labarai daga jihohi shida na arewa maso gabashin Najeriya”.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

BABBAN LABARI

Ni na ajiye aiki ba korata aka yi ba – Baba Impossible

Published

on

By

Tsohom Kwmishinan harkokin addinai na jihar Kano Dr. Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) ya ce shi ya ajiye mukaminsa ba korarsa aka yi ba.

Cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa Dr Muhammad Tahar ya ce tun a ranar 30 ga watan Disamba ya kai wa sakataren gwamnati takardarsa ta ajiye aiki, kuma aka karba aka buga sitamfi aka ba shi nasa kwafin.

Cikin takardar dai (Baba Impossible) ya ce bai bayyana dalilinsa na barin aikin ba.

Sai dai wata sanarwa da Gwamantin Jihar ta fitar mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labaran jihar Malam Muhammad Garba ta ce, Gwamnan Jihar Kano Abdullhai Umar Ganduje ne ya sanar da korar kwamishinan harkokin addini daga mukaminsa.

Kuma tuni aka bayar da sunan Dr. Nazifi Bichi a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Sanarwar ta ce “an kori kwamishinan ne saboda halin rashin da’a da yake nuna wa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati mai rike da mukami.

“An same shi yana gudanar da al’amuran ofishinsa a matsayin sana’a ta kashin kansa, har ma ya kan rage kwanakin aiki ga ma’aikatan ma’aikatar, banda ranakun Laraba da Juma’a.”

Kwamishinan ya kara da cewa baya ga gudanar da aiki ba tare da tuntubar juna ba, Baba Impossible baya biyayya ga gwamnati.

Continue Reading

BABBAN LABARI

Kotu ta yankewa Sheikh Abduljabbar hukunci

Published

on

By

Bayan samun sa da laifin yin kalaman batanci ga Annabi S A W kotun shari’ar musulunci dake zamanta a Kofar kudu karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola kotun ta yankewa malamain hukunci.

Kotu ta yankewa Shekh Abduljabar Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, tare da kwace dukkanin litattafan da ya gabatarwa da kotu, da kwace masallatansa guda biyu, tare da harmta saka hoto da karatunsa a kowace kafar sadarwa.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta kotu tace ta tabbatar Abduljabbar ya yi batanci ga Ma’aiki sannan Kuma ya gaza gabatarwa kotu hujjojin da zasu gamsar da ita ikirarinsa na cewa a cikin litattafai ya ga abubun da ya fada akan Ma’aiki S A W.

Continue Reading

BABBAN LABARI

Da Ɗumi Ɗumi: KOTUN DAUKAKA KARA ZAMAN FARKO.

Published

on

By

A gobe litinin 14 Nuwamba, 2022 kotun daukaka Kara da ke Jimeta zata fara sauraron Kara da ke gabanta na rashin amincewa da hukuncin kotun Tarayya da ta zartar da cewa Jam’iyar APC batada Dan Takara a sakamakon karar da Nuhu Ribadu ya shigar na kalubalantar nasarar Senator Aishatu Dahiru Ahmed Binani.

A gaban kotun dai tana da koke koke kamar haka:

Na farko: Nuhu ya daukaka Kara Yana kalubalantar hukuncin kotun Tarayya na Justice Abdulaziz Anka. Nuhun ya Nemi kotun Daukaka Kara da ta rushe zaben fidda gwanin Kuma ta haramtawa Senator Binani Takara kana ta umarci Jam’iyar APC ta kasa da gudanar da sabon zaben fidda gwanin.

Na Biyu: Uwar Jam’iyar APC ta kasa ita ma ta garzaya kotun ta na kalubalantar hukuncin kotun baya, inda ta ke rokon kotun daukaka Karar da cewa Babu dalilin Hana ta shiga zaben 2023 domin ta gudanar da zaben fidda gwanin Kuma Senator Binani ita ta lashe zaben. Hasalima uwar Jam’iyar APC ta kasa ta na Neman Alfarman kotun da tayi patali da karar da ke gaban ta na sake zabe ta tabbatar da Senator Binani a matsayin Yar takarar Gomnan ta a karkashin Jam’iyar.

Na uku: Senator Aishatu Binani ita ma ta garzaya kotun tana Mai shaidawa kotun cewa duk wasu sharuda na Takara ta cika. Kuma ta tseya Takaran kamar sauran Yan Takaran. Binani tana Neman kotun ta tabbatar da zabin Delegates da suka Bata Amanar kuri’u 430. Binani na Neman kotun daukaka Karar da tayi watsi da hukuncin Babban kotun Tarayya kuma ta tabbatar da zaben da akayi Wanda Allah ya Bata nasara.

Gobe dai za’a a aza d’amba a kotun daukaka Karar. Muna rokon Allah ya tabbatar da Alkhairi

Adamu Ibraheem Jimeta.
13th Nuwamba, 2022

Continue Reading

BABBAN LABARI

Copyright © 2020 VOA voiceofarewa.ng