Connect with us

BABBAN LABARI

Rigima kan rashin cika alqawari na karba karba a Taraba na cigaba da yin tasiri

Published

on

Lado Salisu Muhammad Garba

Wasu yayan jam iyar PDP dake kudancin Taraba sunyi zanga-zanga lumana tare da yin tattaki a yankin kudanchin Jahar

Mr. Andison Emos na daya daga chikin wanda suka yi zanga zanga 

“Yace sun yi zanga zanga ne don mahukuntan jam’iyar su kirawo manyan jihar Taraba don su tunamusu cewa akwai yarjejeniyar da akayi da su akan mulkin karɓa karɓa na mulkin Gwamna a jihar Taraba 

Domin yanzu haka mulkin na Taraba ta kudu ne yakamata yanzu mulkin yakoma yammacin Taraba ne domin wannan lokachin sune Yakamata sai dai jam’iyar PDP tasake fidda ɗan takara a kudanchin Taraba wanda hakan ya saɓa alƙawarin da akayi dasu

Alhaj Salihu Ahmad haifenfen jihar taraba ne kuma ta yankin taraba ta kudu ya chi wannan lokachin sune anma wasu manya a jihar irinsu 

T Y Dan Juma takum sunyiwa batun kama karya don a cewarsa wadanda suke mulkin ma basu yiwa jihar komaiba shiyasa suke song akawo daga yankin su don ya rufamasu asirin kan abinda sukayi 

A daya hanunkuwa Malam Alhaji shima daga yankin Taraba ta kudu yace wannan rashin adallchi ne kawai T Y  Danjuma keson musu a jihar shiyasa ya rushe wannan batu na karba karba a jihar Taraba anma sukan bazasu amince da wannan lamarin ba

Shikuwa jami’in yada labarai na jami’yar PDP a jihar Taraba cewa yayi batun mulkin karmba karmba a jihar ma basu san da itaba Sabodahaka wanan ba batubane da har zai zama abun magana 

Yanzu dai zasu maida hankaline kawai kan babban zaben mai karatowa a Nigeria 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

BABBAN LABARI

Anbaliya ya tafi da mutum biyu kuma gidaje sama da dari biyu sun rushe a loko dake karamar hukumar song na jihar Adamawa 

Published

on

By

Daga lado salisu Muhammad garba 

Wani matashi wanda Anbaliya ya shafa mai suna Rabiu isiyaku ya shaidawa manema labarai chewa gidaje da shagunan su Akasuwa basu sa yawan asarar da sukayi ba

Akasuwan buhuna kuma Abinchi fiye da buhuna dari uku da hamsin ne suka lalace inji Alhaji ibirahim Alliru shugaban masu sana’ar sai da hasti na karamar hukumar song 

Alhaji musa isa magidanchine a kauyen loko inda abin yafaru yace gidajen su gaba daya ruwa ya rusa basuda ma inda zasu koma sai dai kan kwalta shima don ruwan bai tafi dashibane

Shugaban karamar hukumar song hon gidado Abdulsalam zasu yi mai yiwuwa kan wannan batun na Anbaliya don a halinyanzu mazauna yankin na cikin wani mawuyachin hali sakamakon wanan Anbaliyan da yafaru 

Continue Reading

BABBAN LABARI

Babban Sufeton ‘Yan-sandan Najeriya ya haramta amfani da lambar mota ta musamman ta tsaro Usman Alkali Bab

Published

on

By

Shugaban ‘yan-sandan ya bayar da umarnin kwace lambar a ko’ina a NajeriyaImage caption: Shugaban ‘yan-sandan ya bayar da umarnin kwace lambar a ko’ina a Najeriya
Babban Sufeton ‘yan-sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin hana amfani da lambar mota ta musamman ta tsaro wadda ake wa lakabi da SPY, a duk fadin kasar.

Umarnin ya biyo bayan irin matakan da shugaban ‘yan-sandan ke dauka na inganta tsaro da dakatar da yadda daidaikun mutane ke fakewa da wannan lambar mota su rika keta dokokin amfani da titi da sauran ka’idoji, kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga kakakin rundunar na kasa CSP Olumuyiwa Adejobi ta bayyana.

Sanarwar ta ce daga yanzu an haramta wa duk wata mota amfani da irin wannan lamba a ko’ina a fadin Najeriya.

Tare da umartar kwamishinonin ‘yan-sanda na jihohin kasar 36 da Abuja, da mataimakan sufeto janar na ‘yan sanda da su tabbatar da bin umarnin.

Shugaban ‘yan-sandan ya kuma umarci duk ‘yan-sanda da sauran jami’an tsaro da ke aiki da manyan mutane masu amfani da motocin da ke da irin wannan lamba, su tabbatar da bin umarnin ko kuma su fuskanci hadarin kamasu kan kin bin umarnin.

Dokar ta bukaci a kwace dukkanin irin wannan lamba a ko’ina a kasar.

Continue Reading

BABBAN LABARI

Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Nasarawa a majalisar wakilai ta kasa, Hon. Nassir Ali Ahmed ya taya al’ummar jihar Kano murnar bikin Sallah Babba.

Published

on

By

A wata sanarwa da dan majalisar tarayya ya fitar a ranar Lahadin, ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da lokacin bikin Sallah wajen yin addu’ar samun zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

Hon. Nassir Ali Ahmed ya tabbatar wa al’ummar mazabar sa cewa nasarorin da ya samu a wakilcin da yake yi musu ya same su ne bisak jajircewar sa wajen ganin sun samu wakilcin da ya dace a zauren majalisar.

Ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su kiyaye kyawawan dabi’un Musulunci wanda ya ya koya wa mabiyansa ta yadda za su zauna lafiya ba kawai da ‘yan uwa musulmi ba, har ma mabiya sauran addinai.

Hon Nassir Ali Ahmed ya kara da cewa, ba za a iya samun zaman lafiya da hadin kai a Najeriya ba, in ba tare da hakuri a tsakanin mabiya manyan addinai biyu na Musulunci da Kirista ba.

Bugu da kari, ya bukaci al’ummar musulmi da su rika nuna kauna da taimakawa ga makwabtansu da sauran jama’a, yayin da suke gudanar da bukukuwa irin wadannan masu muhimmanci a rayuwarsu.

Ahmed ya kuma yi fatan wannan lokaci na Sallah ya zama silar samun albarka, zaman lafiya, wadata da aminci ga ‘yan Nijeriya ganin cewa idan aka yi addu’a a wadannan kwanaki kalubalen da kasar nan ke fuskanta za su zama tarihi.

Continue Reading

BABBAN LABARI

Copyright © 2020 VOA voiceofarewa.ng