Daga Abubakar Halidu
Yanzu haka a wani sabon yunkuri na samarwa matasa ayyukan yi da kuma dogaro da kai, gwamnatin jihar Adamawa ta buɗe shafin tattara bayanai na matasa masu fasaha, ciki harda ƙungiyoyin mata masu sana’o’i domin tallafa musu da jari.
Wannan sabon shiri dai na karkashin ma’aikatar samar da ayyukanyi da cigaba na jahar Adamawa, kuma tuni har an a buɗe shafin domin matasa maza da mata waɗanda basa aikin gwamnati su cika bayanan su.
Shafin dai an buɗe shi a watan mayu 2020, wanda ya yi makonni, inda aka ɗauki bayanan waɗanda suka gama makaranta kama daga sakandare, makarantar gaba da sakandare, da ma Jami’a, har da ma masu basira da basu gama makaranta ba, da masu buƙata ta musamman.
Da yake jawabi yayin taron ganawa da kungiyoyi, Kwamishinan ma’aikatar samar da ayyukanyi da cigaba na jahar Adamawa, Hon. Iliya James, ya ce, “shafin an buɗe ne ga masu shekaru 18 zuwa 45 a jahar.
“Wanna dai gwamnati ta kawo shi ne, don koyar wa matasa sana’o’i daban-daban a makarantu da ake koyar da sana’o’i da sauran wasu wurare,” a cewar sa.
James ya bayyana cewa taron an yi shi ne da nufin ganawa da jami’an na hukumomin raya ƙananan ƴan kasuwa da masana’antu na tarayya (SMEDAN) da ta Jaha, domin ƙarin haske akan shirin tallafin.

A don haka ne kwamishinan ya ƙirayi matasa da su yi ƙokarin cika bayanan su a wani shiri na tallafawa matasa na National Youth Investment Funds wanda aka buɗe ranar 14/10/2020 don samun shiga tsarin tallafi na kuɗi daga gwamnati.
Yayin da yake jawabi akan wanda zai iya cin gajiyar tsarin tallafawa ƙananan ƴan kasuwa da masu ƙananan masana’antu SME’s, Mustapha Ali-Gana ya ce.
“Duk wata ƙungiya ta ƴan kasuwa da take da rijista da corporate Affairs Commission (CAC) da kuma SMEDAN to tana da damar cin gajiyar wanna tasiri na tallafin amman banda ƙungiyoyi na shafukan sada zumunta.”
“Sannan babu wata rijista da ake gudanarwa a kan teburi da sunan SME’s ko SMEDAN a halin yanzu, duk a kan yanar gizo ake yi,”
Mustapha ya kara da cewa, “mutane su gane cewa takardan shaida da suke da shi na SMEDAN, akwai lambobi na musamman akan takardar da aka turawa kowa bayan ya cika, da ita zaku yi amfani wajen cika tsarin Survival Funds wadda ake cikawa a halin yanzu.”
7 Comments