Connect with us

BABBAN LABARI

Sojoji da CJTF sun ceto wasu manoma daga hannun yan Boko Haram a jihar Borno

Published

on

 

Rahotanni dake shigowa yanzu na cewa sojojin kundunbala da mayakan Civilian JTF sun kubutar da mutanen kauyen Zabarmari manoman shinkafa a kalla 200 daga ‘yan ta’addan Boko Haram

 

Idan ba’a manta ba, ranar lahadi da ta gabata ne ‘yan ta’addan Boko Haram suka yiwa mutanen Zabarmari 43 kisan gilla ta hanyar yankan rago, sannan suka tafi da daruruwan mutane jeji.

 

BABBAN LABARI

Da Ɗumi Ɗumi: KOTUN DAUKAKA KARA ZAMAN FARKO.

Published

on

By

A gobe litinin 14 Nuwamba, 2022 kotun daukaka Kara da ke Jimeta zata fara sauraron Kara da ke gabanta na rashin amincewa da hukuncin kotun Tarayya da ta zartar da cewa Jam’iyar APC batada Dan Takara a sakamakon karar da Nuhu Ribadu ya shigar na kalubalantar nasarar Senator Aishatu Dahiru Ahmed Binani.

A gaban kotun dai tana da koke koke kamar haka:

Na farko: Nuhu ya daukaka Kara Yana kalubalantar hukuncin kotun Tarayya na Justice Abdulaziz Anka. Nuhun ya Nemi kotun Daukaka Kara da ta rushe zaben fidda gwanin Kuma ta haramtawa Senator Binani Takara kana ta umarci Jam’iyar APC ta kasa da gudanar da sabon zaben fidda gwanin.

Na Biyu: Uwar Jam’iyar APC ta kasa ita ma ta garzaya kotun ta na kalubalantar hukuncin kotun baya, inda ta ke rokon kotun daukaka Karar da cewa Babu dalilin Hana ta shiga zaben 2023 domin ta gudanar da zaben fidda gwanin Kuma Senator Binani ita ta lashe zaben. Hasalima uwar Jam’iyar APC ta kasa ta na Neman Alfarman kotun da tayi patali da karar da ke gaban ta na sake zabe ta tabbatar da Senator Binani a matsayin Yar takarar Gomnan ta a karkashin Jam’iyar.

Na uku: Senator Aishatu Binani ita ma ta garzaya kotun tana Mai shaidawa kotun cewa duk wasu sharuda na Takara ta cika. Kuma ta tseya Takaran kamar sauran Yan Takaran. Binani tana Neman kotun ta tabbatar da zabin Delegates da suka Bata Amanar kuri’u 430. Binani na Neman kotun daukaka Karar da tayi watsi da hukuncin Babban kotun Tarayya kuma ta tabbatar da zaben da akayi Wanda Allah ya Bata nasara.

Gobe dai za’a a aza d’amba a kotun daukaka Karar. Muna rokon Allah ya tabbatar da Alkhairi

Adamu Ibraheem Jimeta.
13th Nuwamba, 2022

Continue Reading

BABBAN LABARI

Buɗe kasuwar shanu a Gamborun Ngala yaja hankalin yan kasuwa Shanu a jahar Adamawa

Published

on

By

Gwamnatin jahar Borno dake Arewa maso gabashin Nijeriya ta buɗe wani babban kasuwar Shanu na garin Gamborun Ngala dake Maiduguri a jahar Borno

Dama dai an rufe kasuwar shanun ne tun a lokacin da Boko Haram ke cin karen su babu babba ka a yankunan Arewa maso gabashin Nijeriya sai dai cikin ikon Allah an samu sauƙin al’amarin hakan yasa Gwamnatin Jahar Barno tayi nazari ƙarƙashin Gwamna Baba gaana Umar Zulum

Ya maida hankali tare da samun nasara buɗe kasuwar duba da irin tallafawa al’umma jahar da kasuwar take yi yasa ya bude kasuwar a jiya kuma tafara haɗa jama’a daga buɗe kasuwar

To sai dai bude wannan kasuwar ya shafi manyan kasuwannin Shanu da ake taƙama da dasu a jahar Adamawa kama daga kasuwar Shanu ta garin Mubi dakuma na Ngurore, kasancewar manyan kasuwannin nada kyakkyawar alaƙa ta kasuwanci a tsakaninsu

Wanda akasari ma yan kasuwar shunu da sukayi hijira daga Maiduguri zuwa Adamawa yanzu haka dai sunfara ƙunshe kayan su dan komawa kasuwa Gamboru Ngala, inda suke tada motar shanu guda a kan kudin haraji Naira dubu huɗu 4000 sabanin dubu saba’in da Biyar 75.000 a jahar Adamawa

Bayan karin da aka samu na biyan kudin haraji kasuwar Dabbobi a jahar Adamawa daga Naira 200 zuwa 500 daga dari 500 kuma zuwa 5000 sai dai bayan samun yewan korafi daga gun yan kasuwar sai Gwamantin jahar ta maidashi Naira dubu uku 3000

Continue Reading

BABBAN LABARI

HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAN NA JAHAR ADAMAWA TA MAIDAWA DUKKAN ALHAZAN DA SUKA BIYA KUDIN HAJJIN SU NA 2022 SAMA DA MILIYAN BIYU DA DUBU DARI BIYAR CHANJIN.

Published

on

By

A jiya Laraba 19/10/2022 Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazan na Jahar Adamawa Mallam ABUBAKAR SALIHU ya mika takardun kudi na Draft da Cheque ga jami’an kula da aikin Hajji na kananan hukumomi 21 dake wannan.

Idan ba’a Manta ba,maniyatan na Jahar Adamawa wadanda sukayi aikin Hajjin 2022 wasu daga cikin su sun biya sama da Naira Miliyan biyu da dubu dari biyar wasu kuma sun biya daidai yadda Gwamnati ta baiyana kudin aikin Hajjin na 2022 wato sama da Miliyan biyu da dubu dari hudu.

Mallam ABUBAKAR SALIHU yace wadanda suka biya sama da Miliyan biyu da dubu dari biyar kadai za’a maidawa chanjin su da kuma wadanda basu samu zuwa aikin Hajjin ba,kuma suna bukatan Hukumar ta maida musu kudin su.

Shugaban Hukumar Mallam Bappari Umar Kem wanda shine ya jagoranci mika takardun kudi ga jami’an kula da aikin Hajji na kananan hukumomi dan su rabawa Alhazan ya kiraye su dasu tabbatar sun mika su ga dukkan Alhazan da suka tabbatar sun biya kudin aikin Hajjin su sama da Miliyan biyu da dubu dari biyar.

Shima dayake jawabin godiya Shugaban jami’an kula da aikin Hajji na kananan hukumomi 21 Alh Ya’u Gambo ya JINJINAWA SARKI TURAWA GURIN wato Babban Sakataren Hukumar Mallam ABUBAKAR SALIHU da irin namijin kokari da yayi na tabbatar da cewa ko wane Alhaji an mika mishi wannan takarda na Draft dan ya samu kudin shi a asusun bankin shi daidai.

Taron an gudanar dashi ne a Babban dakin taro na Hukumar Jin Dadin Alhazan na Jahar Adamawa indan dukkan Manyan jami’an Hukumar suka hallara tare da dukkan jami’an kula da aikin Hajji na kananan hukumomi 21 dake wannan jaha.

Continue Reading

BABBAN LABARI

Copyright © 2020 VOA voiceofarewa.ng