Sumba na iya zama abu mai kyau na bayyana soyayya, amma ko kun san a duk lokacin da kuka sumbaci abokin tarayya, me kuke bayarwa?
Wani lokaci mu mutane muna tunanin ƙara dankon ƙauna ne da soyayya, amma kuma akwai abin da watakila ba mu fahimta ba… ta hanyar sumbata, muna yaɗa ƙwayoyin cuta da dama.
Ko da yake ba lallai ya zama haka ba, tsarin yadda aka halicci baki yana da rikitarwa kuma yana iya adana nau’ikan ƙwayoyin cuta har 700 waɗanda za su iya rayuwa.
Siffar tsarin bakin yana bai wa yawu damar samar da matsakaicin zafin jiki da kuma wadataccen abinci mai gina jiki, don haka wannan yanayin yana taimaka wa ƙwayoyin cuta su hayayyafa da girma.
Tun da bakin ya cika da ƙwayoyin cuta, a bayyane yake cewa za mu iya watsa waɗannan ƙwayoyin idan muka yi sumba.
Gaskiyar ita ce, a cewar wani binciken da ɗalibai a Netherlands suka yi, yana yiwuwa idan ka sumbaci wani na tsawon daƙiƙa 10 a rana, za ka iya yada ƙwayoyin cuta har miliyan 80.
Wadanne kwayoyin cuta ke shiga bakinku?
Kwayar cutar da ke cikin baki sunanta ‘microbiota’ wacce dama can take baki tun daga haihuwa.
Tana canzawa dangane da abin da muke ci, ko magani ne ko a’a, muna da tsabta ko kuma muna shan sigari.
Shekarunmu da yanayin kwayoyin halitta suna shafar tsarin waɗannan ‘microbiota’.
Duk da wannan, ƙwayoyin halittar da ke zaune a bakin ɗan adam suna da fa’idoji da yawa.
Mafi yawa dai shi ne yana taimakawa wajen hana ƙwayoyin cuta samuwa, yana tallafawa garkuwar jiki da tsarin narkewar abinci tare da daidaita hawan jini.
Waɗannan ƙwayoyin cuta suna rayuwa tare kuma a sassa daban -daban na baki, kuma suna hada abin da ake kira ‘biofilms’.
Suna mannewa da bangon wurare daban-daban a cikin baki musamman a kan wani bangare da ake ce wa ”substrate” saboda haka suna samun kariya daga sindarai kamar na ‘antibodies’ da ke aiki da garkuwar jiki.
Ire -iren wadannan kwayoyin cuta suna farawa ne daga hakora, dasashi ko harshe.
A wasu wuraren kamar kumatu, babu lokacin da za a samar da waɗannan ‘biofilms’ saboda sabunta ƙwayoyin ‘mucosa’ yana faruwa cikin sauri.
Kusan kowane bangare na baki yana dauke da isashshen oxygen da yanayi na sinadaran abinci, yanayin da ke sa tarin kwayoyin cuta ya sauya a kai a kai.
Irin wannan kwayoyin cuta ba iri ɗaya ba ko da a haƙori ɗaya ne, amma ɗayan yana gaba da bayan hakori ɗaya.
Wannan bambancin yana da girma sosai don haka ‘microbiota’ na harshenku na iya zama kamar baƙo ga hakoran ku.
Akwai abubuwa da yawa da suka danganci sumbata
Kusancin da ake buƙata yayin sumbata ya na taimakawa ko ba da damar ƙwayoyin cuta su tashi daga baki ɗaya zuwa wani.
Za mu iya kawar da yawancinsu ba tare da mun sani ba.
Damar kwayoyin cuta su rayu a baki ya danganta ne da yadda za su dace da inda suke.
Bugu da kari, tsarin garkuwar jiki, ba ya taimakawa wajen sauƙaƙe shi, tun da miyau na haduwa da kwayoyin ‘antibody’ da ake kira IgA, wanda majina ke samarwa, wanda ke ƙoƙarin hana hulɗa da ƙwayoyin cuta.
A takaice, mutanen da ke da gibi a tsarin haƙoransu a cikin baki, ba su da yawan wadannan ‘antibodies’ din ba.
Don haka, lokacin da kuka sumbaci mutum, kuna karɓar ƙwayoyin cuta da yawa daga mutumin da kuke sumbata, yawancin waɗannan ƙwayoyin suna shiga cikin hanji kai tsaye.
Amma wasu suna mannewa a baki.
Tasirin wannan shi ne yana da wuya ƙwayoyin cuta su zauna a baki bayan sumba, amma dole ne ku yi hankali saboda akwai ƙwayoyin cuta waɗanda ba su isa su ɓoye ta cikin ‘microbiota’ ba.
Haɗarin irin waɗannan ƙwayoyin cuta
‘Biofilm’ da ƙwayoyin cuta ke samarwa a hakora ana ce masa murufin haƙori a cikin harshe na yau da kullun.
Wani lokaci yana da wuyar kawar da shi. Kwayoyin cuta suna amfani da sukari a cikin abinci kuma suna samar da sinadarai masu yawa.
Wannan yanayin yana sa sindarain da ke lullube a kan hakori mai suna enamel ɗin haƙora ya lalace kuma ya haifar da lalacewar haƙora.
Don haka shan sukari yana da alaƙa kai tsaye da lalacewar haƙora ko ramukan cikin hakori. Wannan ba sabon abu ba ne.
Bisa bayanan da aka tattara, an samu ƙaruwa sosai a lalacewar haƙora, bayan an cire haraji kan sukari a Ingila, kuma wannan ya zama ruwan dare.
Daya daga cikin kwayoyin da aka gano yana haifar da mafi yawan matsaloli sunanata ‘Streptococcus mutans’ da wani nau’i na Lactobacillus.
Za mu iya kawar da waɗannan ƙwayoyin cuta?
Idan ba a cire kurajen ko kumburin daga hakoran ba, zai haifar da kumburi a dasashi kuma ya haddasa wata cuta da ake kira ‘periodontitis’.
A gefe guda kuma, kada mu manta cewa ƙwayoyin cuta da yawa na wannan nau’in ‘microbiota’ a cikin baki suna da alaƙa da halitosis (mummunan warin baki da tarin ƙwayoyin cuta ke haifarwa).
Waɗannan ƙwayoyin cuta galibi suna rayuwa cikin harshe kuma suna samar da abubuwan da ke motsa ƙona sinadarin protein. Don haka, tsafta tana da mahimmanci wajen rage kamuwa da cututtuka na baki.
Ta hanyar goge bayan kowane abinci, yana taimakawa cire fim ɗin biofilm daga ƙyallen haƙora da ƙwayoyin cuta.
Bugu da ƙari, yayin da kuke goge hakora, kuna jawo ƙwayoyin cuta waɗanda ke buƙatar iskar oxygen don su girma, wanda abu ne mai kyau.
Ya kamata ku yi buroshi da wanke harshenku.
Ku ji daɗin rayuwa … kuma ku rarraba ‘microbiota’
Gabaɗaya, ma’auratan da ke cikin ingantacciyar soyayya suna samun kansu da ƙwayoyin cuta iri ɗaya ko masu kama da na juna.
Suna kara sumbatar juna, suna kara ba junansu kwayoyin cuta da kuma kwayoyin cutar suna kara kamanceceniya.
Wannan na iya zama abin jan hankali ga masoya, amma yana da nasa illolin.
Lokaci na tafiya, mutanen da ke fama da cututtukan baki na iya yada wa matansu ko mazansu cututtukan.
A halin yanzu, ana ci gaba da bincike don samar da wani abu da za a sanya rika sanya wa a baki don taimakawa hana lalacewar haƙora.
Wani binciken da aka yi a baya a Valencia, ya nuna cewa yana da sakamako mai kyau.
Sumba tana taimakawa wajen samar da soyayya mai ƙarfi, tana motsa rai kuma ta na ƙara ƙarfin soyayya tsakanin masoyayya. La’akari da duk abin da muka gani a cikin wannan maƙala, ana ba ku shawarar ku yi taka-tsan-tsan wajen zaɓar wanda za ku iya kulla alaƙa da shi da musanya ‘microbes’.
Recent Comments