Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun kashe sama da mutum 40 a jerin hare-hare da suka kai a wasu kauyukan jihar.
Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da kai harin, amma ta shaida wa BBC Hausa cewa mutum 35 aka kashe.
Lamarin ya faru ne a ƙauyuka fiye da biyar da ke karamar hukumar Maradun da ranar Alhamis sai dai bayanai ba su fito ba sai Juma’a.
Ganau sun shaida wa BBC cewa maharan sun je ƙauyukan Gidan Adamu da Gidan Maidaji da Bauci da Wari da Kyara da Gidan Maidawa kan babura sannan suka buɗe wuta.
Lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum 42, a cewar wani mutum da muka tattauna da shi.
“Wannan lamari ya faru ne a jiya Alhamis tun daga karfe 12 na rana har zuwa bayan la’asar, a lokacin da ‘yan bindigar suka shiga shiyyar kan babura sama da 100,” in ji wani da ya shaida lamarin.
Wannan hari na zuwa ne kwana biyu kacal bayan da ƴn bindiga suka kashe mutum 18 a jihar Katsina.
Sannan kuma waɗannan hare-hare duk sun faru ne a yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin cetofiye da ɗalibai 100 da aka sace a wata makarantar kwana a jihar Kaduna.
Satar ɗaliban ita ce ta baya-baya cikin lamari irin sa da yake neman zama ruwan dare a arewacin Najeriya.
Recent Comments